Wasu hanyoyi da ya kamata kowa ya sani da ake bi wurin aikata magudin zabe a yanzu

Wasu hanyoyi da ya kamata kowa ya sani da ake bi wurin aikata magudin zabe a yanzu

Hukumar kula da tsare-tsaren zabe ta nahiyar Afrika ta bayyana sayen kuri'a da 'yan siyasa ke yi a matsayin wata sabuwar hanya da aka fito da ita a Najeriya ta aikata magudin zabe a Najeriya

Wasu hanyoyi da ya kamata kowa ya sani da ake bi wurin aikata magudin zabe a yanzu

Wasu hanyoyi da ya kamata kowa ya sani da ake bi wurin aikata magudin zabe a yanzu

Hukumar kula da tsare-tsaren zabe ta nahiyar Afrika ta bayyana sayen kuri'a da 'yan siyasa ke yi a matsayin wata sabuwar hanya da aka fito da ita a Najeriya ta aikata magudin zabe a Najeriya.

Cynthia Mbamalu, Daraktar hukumar ita ce ta bayyana hakan a yau Larabar nan a garin Osogbo, a wani shiri da taje yi da manema labarai akan zaben da za'a gabatar a jihar Osun ranar 22 ga watan Satumbar nan.

Mbamalu ta ce sayen kuri'a ya zama tamkar ruwan dare a Najeriya, inda ta kara da cewa dolene a dauki dukkanin matakin da ya kamata don kawo karshen matsalar.

DUBA WANNAN: Shehu Sani ya bayyana hanyoyi biyar da gwamnatin Buhari zata tafi da wadanda suka bar jam'iyyar APC

Ta ce, "A halin yanzu siyasar Najeriya ta zama iya yawan kudin da ka bayar iya yawan kuri'un da zaka samu, kuma hakan ba karamin matsala bane a tsarin zabe a kasar nan dama nahiyar nan baki daya."

Mbamalu ta ce tun lokacin da aka fito da tsarin amfani da na'ura mai kwakwalwa wurin jefa kuri'a, magudi ya ragu sosai, amma yanzu 'yan siyasar sun samu wata sabuwar hanya ta sayen masu jefa kuri'ar da kudi.

Ta ce ranar da za'a gabatar da zaben jihar Osun hukumar ta su zata aiko da ma'aikata mutum 500 a fadin mazabu 250 dake fadin jihar.

Mbamalu ta kara da cewa hukumar ta su kuma zata yi iya bakin kokarin ta wurin wayar da kan jama'a akan harkar zabe. Ta ce babban abinda kungiyar su ta ke kokarin kawowa shine ta tabbatar da an gabatar da tsafe cikin kwanciyar hankali ba tare da magudi ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel