Gwamna Masari ya caccaki Shugabannin Arewa akan al'amurran da suka shafi Ilimi

Gwamna Masari ya caccaki Shugabannin Arewa akan al'amurran da suka shafi Ilimi

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya yi watsi tare da kaca-kaca dangane da shirye-shirye da tsare-tsaren shugabannin Arewa akan harkokin ilimi, inda ya nemi a tabbatar da samar da bukatun ilimi domin yaransu su ci gajiya.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, Masari ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye dalibai karo na ashirin da aka gudanar a Kwalejin nazarin Larabci da addini Islama dake garin Daura.

Gwamnan ya yi Allah wadai dangane da yadda yankunan Arewa ke dogaro da gwamnatin tarayya ko jiha wajen samar da ilimi, inda ya bayar da misali karn yadda jihar Legas ta yi zarra ta fuskar ilmantarwa sakamakon mafi karancin adadin makarantun gwamnati dake fadin jihar.

Gwamna Masari ya caccaki Shugabannin Arewa akan tsare-tsaren Ilimi

Gwamna Masari ya caccaki Shugabannin Arewa akan tsare-tsaren Ilimi

A sanadiyar haka gwamnan ya yi kira ga makarantu masu zaman kansu akan kauracewa dogaro da gwamnati wajen gudanar da al'amurransu, inda ya ce gwamnati ba ta bayar da muhimmiyar kulawa a gare su sabanin makarantu masu zaman kansu.

Gwamnan ya sha alwashin tallafawa wannan kwalejin ilimi tare da daukar nauyin wasu dalibai shida da suka nuna zakakuranci a faggen karatun su.

KARANTA KUMA: Ofishin Jakadancin Amurka ya nemi 'Yan Najeriya akan su yi koyi da Limamin da ceci Kiristoci 300 a jihar Filato

A nasa jawaban, babban bako na musamman a wannan taro, Sarkin Daura Alhaji Umar Farouk Umar, ya yabawa wadanda suka assasa wannan kwalejin ilimi shekaru ashirin da suka gabata.

Legit.ng ta fahimci cewa, shugaban jami'ar Ahmadu Bello, Farfesa Ibrahim Garba, ya tsawaita batutuwan sa musamman kan hada gwiwa tsakanin jami'ar sa da kuma babbar kwalejin ta Garin Daura domin inganta nasabar ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel