'Yan sanda a Kano sun bazama neman wadanda su kayi fyade yarinya ga yarinya 'yar shekara 3

'Yan sanda a Kano sun bazama neman wadanda su kayi fyade yarinya ga yarinya 'yar shekara 3

- Wata karamar yarinya 'yar shekara 3 ta sheka barzahu bayan anyi mata fyade a Kano

- Sai dai tuni jami'an 'yan sanda sun kai farmaki har sun damke mutane 9 domin fara bincike

- Kakakin rundunar Magaji Musa Majiya ya sha alwashin zakulo masu lafin nan da 'yan kwanaki kadan masu zuwa

An samu gawar wata yarinya mai Khadija Abubakar Abdullahi ‘yar shekara 3 da haihuwa a wani ofishi dake makarantar Khairat dake Walambe, bayan kwanaki hudu da bacewarta.

Binciken ‘yan sanda ya tabbatar da cewa fyade aka yiwa yarinyar sakamakon gwajin da aka yi tare da samun jini daga wasu sassan al’aurarta.

'Yan sanda a Kano sun bazama neman wadanda suka yiwa 'yar karamar yarinya fyade

'Yan sanda a Kano sun bazama neman wadanda suka yiwa 'yar karamar yarinya fyade

Kwanaki hudu da bacewar Khadija bayan da suka tafi makarantar Khairat wanda dama a nan mahaifiyarta ke koyarwa.

KU KARANTA: Labarin dan Najeriyan da ya cirewa wata mai ciki gyambo sannan ya mayar da dan cikinta ya dinke

Bayan majiyarmu ta tuntubi kakakin hukumar ‘yan sanda na Kano, ASP Magaji Musa Majia, ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace ya zuwa yanzu an kama malaman makarantar har su tara wadanda ake zargin ko suna da hannu a ciki.

Majia ya tabbatarwa jama'a cewa cikin kwanaki hudu zasu fito da duk wanda ya aikata wannan mummunar ta'asa.

'Yan sanda a Kano sun bazama neman wadanda suka yiwa 'yar karamar yarinya fyade

'Yan sanda a Kano sun bazama neman wadanda suka yiwa 'yar karamar yarinya fyade

Yayin zantawarsa da jami'an ‘yan sanda, mahaifin yarinya mai suna Alhaji Abubakar Abdullahi wanda akewa lakabi da IBB, yace ya samu yar tasa kwance cikin jini ba kaya a jikinta, kuma duk wasu sassan jikinta cike yake da jini musamman duburarta.

"Halin da muka tsinci ‘yarmu a ciki shi ya tabbatar mana da cewa fyade aka yi mata wanda ko jikinta ba mu kai ga iya tabawa ba".

"Gawar ta fara wari, don haka a nan take na kira ‘yan sanda domin su yi bincike, kuma bayan kammala binciken nasu suka dawo mana da gawar domin yi mata sutura kamar yadda addini ya tanada.

Duk da cewa ta Khadija ta kare amma ina so a yi hukunci domin babu wanda yasan gobe wadda za’a yiwa haka".

"Mahaifiyarta tana koyarwa a makarantar, amma ranar basu tafi tare ba saboda bata jin dadi. Bayan an tashi daga makarantar da misalin karfe 5:30pm na yamma, sai ‘yan uwanta da suka tafi suka dawo gida ba tare da ita ba, tare da shaida mana cewa basu san inda ta shiga ba" a cewar mahaifin marigayya Khadija.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel