Abinda ficewar Saraki ke nufi ga APC - Farfesa Sagay

Abinda ficewar Saraki ke nufi ga APC - Farfesa Sagay

Shugaban kwamitin bawa shugaba Buhari shawarar a kan yaki da cin hanci, Farfesa Itse Sagay, ya bayyana ficewar Saraki daga APC a matsayin abun alheri ga jam'iyyar.

Ya bayyana cewar tun da Saraki ya zama shugaban majalisar dattijai yake cin dunduniyar jam'iyyar APC da gwamnatin ta. Ya kara da cewar ficewarsa zata karawa jam'iyyar karfi ne kawai.

"Tsarki ya samu APC. A wurina, ficewar Saraki ta kawo karshen fitar mugunya dake cikin jam'iyyar APC, yanzu zata karfi saboda babu dabaibaye mata kafafun tafiya.

Abinda ficewar Saraki ke nufi ga APC - Farfesa Sagay

Farfesa Sagay

"Dama tun da ya zama shugaban majalisar dattijai yake yake kokarin rusa APC. Ko kafin ya kai ga zama shugaban majalisar dattijai saida ya sayar da kujerar mataimakinsa ga PDP. Ya zamar wa APC dan kuka. Ficewar sa ita ce mafi alheri ga jam'iyyar," a cewar Sagay.

DUBA WANNAN: Da na koma PDP gara na hakura da siyasa - Tsohon gwamnan APC

A satin da ya gabata ne wasu mambobin majalisar dattijai 15 da na majalisar wakilai 37 suka fita daga jam'iyyar APC tare da tsallakawa zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

An dade da bayyana cewar shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, da takwaransa na majalisar wakilai, Yakubu Dogara, zasu fice daga jam'iyyar APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel