Al'umma masu son cigaba: Sun tarawa kasar su taimakon dala miliyan 41 a cikin wata biyu, don ta biya bashin da ake binta

Al'umma masu son cigaba: Sun tarawa kasar su taimakon dala miliyan 41 a cikin wata biyu, don ta biya bashin da ake binta

Al'ummar kasar Malaysia sunyi wani abin mamaki, inda suka hada karfi da karfe suka tara taimakon sama da dala miliyan 41 ga gwamnatin kasar domin ta biya wasu basussuka da kasashe waje suke bin kasar

Al'umma masu son cigaba: Sun tarawa kasar su taimakon dala miliyan 41 a cikin wata biyu, don ta biya bashin da ake binta

Al'umma masu son cigaba: Sun tarawa kasar su taimakon dala miliyan 41 a cikin wata biyu, don ta biya bashin da ake binta

Al'ummar kasar Malaysia sunyi wani abin mamaki, inda suka hada karfi da karfe suka tara taimakon sama da dala miliyan 41 ga gwamnatin kasar domin ta biya wasu basussuka da kasashe waje suke bin kasar.

Gwamnatin kasar dai ta bude wani asusu mai suna "Kudaden Farfadowa".

DUBA WANNAN: Shehu Sani ya bayyana hanyoyi biyar da gwamnatin Buhari zata tafi da wadanda suka bar jam'iyyar APC

Hukumar tattalin arziki ta kasar Malaysiya tace, a cikin watanni biyu kacal al'ummar kasar sun tarawa gwamnati taimakon kudi sama da dala miliyan 41.

Ministan kudi Lim Guan Eng yace, kudin da kasar take nema yana da mutukar yawa, amma duk taimakon da jama'a zasu bayar za ayi amfani dashi wurin yiwa kasa aiki.

A ranar 30 ga watan Mayun wannan shekarar ne aka kafa asusun inda a cikin kwanaki uku kacal aka tara sama da dala miliyan 1.76.

Kasar Malaysia ta tarawa kanta bashi har na dala biliyan 252 wanda ta ciyo daga kasashen waje a lokacin mulkin tsohon Firaiministan kasar Najip Razak.

A yanzu haka dai an rage kashi 10 daga cikin albashin ma'aikatan kasar domin tattalin kudade.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel