Shehu Sani ya bayyana hanyoyi biyar da gwamnatin Buhari zata tafi da wadanda suka bar jam'iyyar APC

Shehu Sani ya bayyana hanyoyi biyar da gwamnatin Buhari zata tafi da wadanda suka bar jam'iyyar APC

Sanata mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya shawarci gwamnatin tarayya akan yanda zata zauna da wadanda suka gudu daga jam'iyyar ta APC

Shehu Sani ya bayyana hanyoyi biyar da gwamnatin Buhari zata bi da wadanda suka bar jam'iyyar APC

Shehu Sani ya bayyana hanyoyi biyar da gwamnatin Buhari zata bi da wadanda suka bar jam'iyyar APC

A kokarin da jam'iyyar APC mai mulki take domin ganin komai ya dai - daita dangane da canja sheka da wasu manya daga cikin jam'iyyar suke yi, Sanata mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya shawarci gwamnatin tarayya akan yanda zata zauna da wadanda suka gudu daga jam'iyyar ta APC.

Sanatan yayi bayanin a shafin sa na Facebook yau Larabar nan da safe, inda ya kawo shawara akan yanda jam'iyyun biyu zasu zauna lafiya ba tare da wani tashin - tashina ba.

DUBA WANNAN: Duniya ina zaki damu: Ta gwammace ta aika shi lahira, data bari ya duba wayarta

Ga abinda Sanatan yace:

"Domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin jam'iyya mai ci da kuma jam'iyya mai mulki, ina ganin akwai hanyoyi guda 5 da idan har jam'iyyun suka bi za a samu dai - dai to har zuwa lokacin zabe mai zuwa.

1. Akwai bukatar kowanne bangare su dauka cewar kasa suke yiwa aiki, kuma cigaban kasa ya zamo abu na farko a kowanne bangare.

2. Sannan manya daga cikin mu su girmama duk wani wanda yake da niyyar barin jam'iyyar, sannan kuma kada ayi kokarin cutar da duk wani wanda ya bar jam'iyya.

3. Sannan duk wata jam'iyya mafi rinjaye a majalisa kada ta kawo wani kuduri da zai karya dokar gwamnati, sannan dole a girmama shugaban kasa da duk wani wanda yake makusanci gareshi.

4. Dole ne kowanne bangare su tsayar da duk wani kuduri na ganin an musgunawa wani bangare.

5. Duka bangarorin biyu su hada karfi da karfe wurin ganin an kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan, sannan kuma su bada himma wurin ganin an gabatar da zabe mai zuwa cikin kwanciyar hankali."

Sanata Shehu Sani yana daya daga cikin wadanda ake tunanin zasu canja sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP. Sai dai kuma shi din ya fito ya bayyana cewar baya cikin wannan guguwar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel