Yanzu Yanzu: Mambobin PDP a Kwara sun gudu sun koma APC saboda dawowar Saraki jam’iyyar

Yanzu Yanzu: Mambobin PDP a Kwara sun gudu sun koma APC saboda dawowar Saraki jam’iyyar

Mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Laraba sun sanar da sauya shekarsu zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Cif Rex Olawoye, babban sakatarn labarai na jam’iyyar ya bayyana hakan ga kamfanin dillancinlabaran Najeriya (NAN) a Ilorin.

“Ina sanar da ficewa nadaga jam’iyyar PDP zuwa APC,” inji shi.

Olowoye wadda ya bayyana shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki a matsayin wata “cuta” ya ce mabobin PDP a jhar bazasu iya aiki tare da shi ba.

Yanzu Yanzu: Mambobin PDP a Kwara sun gudu sun koma APC saboda dawowar Saraki jam’iyyar

Yanzu Yanzu: Mambobin PDP a Kwara sun gudu sun koma APC saboda dawowar Saraki jam’iyyar

Olawoye yace sakamakon sauya shekarsa, dukkanin reshen PDP a matakan, mazabu, kananan hukumomi da jiha sun koma APC.

Ya kuma bayyana cewa sun samu tarbamai kyau daga shugabannin APC.

KU KARANA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotu ta bayar da umurnin kama shugaban INEC, Mahmoud

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a ranar Talata ya hadu da magoya bayansa a Ilorin, inda anan ya fada masu cewa ya bar jam’iyyar All Progressives Congress saboda jajircewarsu akan ya aikata hakan da kuma shige masa gaba da Allah yayi.

Ya ci gaba da zargin cewa an nuna wariya ga jihar Kwara wajen nade-naden da gwamnatin APC ke yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel