Fitar Bukola Saraki daga APC ta bar baya da kura a majalisa

Fitar Bukola Saraki daga APC ta bar baya da kura a majalisa

- Bayan fitar shugaban majalisar wakilai daga jam'iyyar APC, an fara ruru wutar tsige shi

- Sanata Abdullahi Adamu ya shaida cewa za suyi duk yadda za suyi don ganin tilar sun sauke Sarakin daga mukaminsa

Biyo bayan ficewar shugaban majalisar dattawa Dakta Abubakar Bukola Saraki daga jam’iyyar APC zuwa PDP, Sanata Abdullahi Adamu yayi kira ga shugaban majalisar akan ya sauka daga mukaminsa.

Fitar Bukola Saraki daga APC ta bar baya da kura a majalisa

Fitar Bukola Saraki daga APC ta bar baya da kura a majalisa

Abdullahi Adamu wanda ya zanta da manema labarai jim kadan da ficewar Sarakin daga APC, ya ce zai yi duk mai yiwuwa domin ganin Sanata Saraki ya sauka daga shugabancin majalisar dattawa.

KU KARANTA: Dambarwar siyasa: An yiwa Tinubu, Oshiomhole da Amaechi wankin babban bargo

Inda ya ce “Saraki ya jefa kansa a tsaka mai wuya, domin kuwa jam’iyyar APC ce ke da rinjaye a zauren majalisun kasar nan, saboda haka matukar yana girmama doka to babu shakka sai ya sauka daga mukaminsa" in ji Abdullahi Adamu.

Ya kuma bayyana cewa bai yi mamakin ficewarsu daga jam’iyyar APC ba, domin kuwa ya dade da fadar cewar hakan zai faru.

A karshe ya tabbatar da cewar ba za su taba barin Saraki ya cigaba da shugabantar majalisar Dattawan ba.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel