Manyan dalilai 10 da suka sabbaba ficewata daga jam’iyyar APC zuwa PDP – Tambuwal

Manyan dalilai 10 da suka sabbaba ficewata daga jam’iyyar APC zuwa PDP – Tambuwal

A ranar Laraba,1 gawatan Agustan ne Gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC da komawarsa zuwa jam’iyyarsa ta baya, jam’iyyar PDP.

Sai a yayin sa Tambuwal ya bayyana ficewar tasa daga APC, ya bayyana wasu manyan laifuka da ya zargi jam’iyyar da tafkawa tun bayan darewarta mulkin Najeriya shekaru uku da suka gabata, bayan ta samu nasarar a zaben 2015.

KU KARANTA: Yansanda sun yi musayar wuta da yan bindiga a Talatar mafara, sun kama 12

Tambuwal yace yana zaman zamansa a matsayinsa na Kaakakin majalisar wakilai, amma ya fice ya koma APC don samar da shugabanci mai kyau, sai ga shi a yau gwamnatin APC na ana nuna wariya tsakanin mutane da rashin adalci wajen rarraba mukamai da ayyukan cigaba.

Manyan dalilai 10 da suka sabbaba ficewata daga jam’iyyar APC zuwa PDP – Tambuwal

Tambuwal

Bugu da kari Tambuwal yace tun bayan yakin Basasar Najeriya, kasar bata taba shiga halin rashin tsaro da rarrabuwar kai ba kamar a mulkin APC, ga matsalar katobara da rashin iya magana akan idan zasu yi raddi akan muhimman matsalolin kasar nan.

“Na tabbata babu kasar da zata cigaba da rashin adalci da gurbataccen shugabanci, kuma dasu ake tafiyar da Najeiya a yanzu haka, ni kuma a nawa bangare na kasa daidaita kaina da irin wannan mulki, don haka na fice daga APC zuwa PDP.” Inji shi.

Sauran hujjojin da suka sabbaba ficewar Tambuwal daga APC sun hada rashin samun manyan ayyuka masu muhimmanci a Sakkwato daga gwamnatin shugaba Buhari, rashin cigaba da muhimman ayyukan gwamnatin tarayya da gwamnatin Buhari ta gada a Sakkwato, da hana jihar Sakkwato muhimman mukamai.

Daga karshe Tambuwal yace matsalar tsaro da suka addabi Sakkwato da Zamfara, kisan Yansanda da Boko Haram, sun nuna APC ta gaza, kamar yadda matsalar rashin samar da aikin yi ga matasa, yunwa da talauci suka tabbatar da haka, duk wadannan dalilan ne suka sanya shi yanke shawarar ficewa daga APC.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel