Yanzu Yanzu: Kotu ta bayar da umurnin kama shugaban INEC, Mahmoud

Yanzu Yanzu: Kotu ta bayar da umurnin kama shugaban INEC, Mahmoud

Justis Stephen Pam na babban kotun tarayya dake Abuja a ranar Laraba tayi umurnin kama shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Yakubu Mahmoud, saboda kin bin umurnin kotu.

Justis Pam ta bayar da umurnin kama Mahmoud ne bayan rashin hallara a kotu don nuna dalilin da zai sa aki kai shi gidan yari bisa zargin raina kotu.

Yanzu Yanzu: Kotu ta bayar da umurnin kama shugaban INEC, Mahmoud

Yanzu Yanzu: Kotu ta bayar da umurnin kama shugaban INEC, Mahmoud

Kotun a yayin da take yanke hukunci, ta bayyana cewa bazata iya ci gaba da yadda da rashin kasancewar wadanda ake tuhuma a kotu ba don amsa shari’a.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Ina ma ace ban taba kasancewa dan APC ba – Kakakin majalisar Kwara ya jagoranci yan majalisa 23 zuwa PDP

Lauyan dake kare Mahmoud, Cif Adegboyega Awomolo (SAN), ya sanar da kotu cewa Mahmoud ba zai iya halartan kotu ba saboda ya tafi ziyarar aiki mai muhimmanci a kasar Mali.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel