Ofishin Jakadancin Amurka ya nemi 'Yan Najeriya akan su yi koyi da Limamin da ceci Kiristoci 300 a jihar Filato

Ofishin Jakadancin Amurka ya nemi 'Yan Najeriya akan su yi koyi da Limamin da ceci Kiristoci 300 a jihar Filato

Ofishin jakadancin kasar Amurka dake Najeriya, ya nemi al'ummar kasar nan akan su mike tsaye wajen koyi da wani Dattijon Limami, Abdullahi Abubakar, da ya ceci Kiristoci 300 daga mahara kauyen Nghar Yelwa dake karamar hukumar Barikin Ladi a jihar Filato.

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya bayyana, ofishin jakadancin ya yi wannan kira ne a ranar Talatar da ta gabata da sanadin wani ma'aikacin, Mista David Young, yayin taron kwanaki uku da aka shirya kan zaman lafiya cikin wani masaukin baki na Crest Hotel dake Jos.

Mista Young yake cewa, ya yi gwagwarmaya da mutanen daban-daban a rayuwar sa amma ko kada bai ta ganin wanda ya sadaukar da rayuwar sa domin ceton wasu kamar yadda wannan Limami ya yi na kare Kiristoci 300 a jihar Filato.

Ofishin Jakadancin Amurka ya nemi 'Yan Najeriya akan su yi koyi da Limamin da ceci Kiristoci 300 a jihar Filato

Ofishin Jakadancin Amurka ya nemi 'Yan Najeriya akan su yi koyi da Limamin da ceci Kiristoci 300 a jihar Filato

Ya ci gaba da cewa, wannan abin son barka da Limamin ya aiwatar kalubale ne a gare mu da ya cacanci daukar izina da koyi wajen sadaukar da rayukan domin tabbatar da zaman lafiya a kwanciyar hankali.

KARANTA KUMA: Sanata Adamu ya bukaci Saraki ya furta cin amanar da ya yiwa Shugaba Buhari

Mista Young ya kara da cewa, ofishin jakadancin da kuma gwamnatin Kasar Amurka sun la'anci wannan kashe-kashe da zubar da jini dake faman aukuwa a sassa daban-daban musamman jihohin Filato, Zamfar, Benuwe da kuma Taraba dake fadin kasar nan.

A yayin da ofishin jakadancin ke ci gaba da kira akan tabbatar da zaman lafiya da la'antar ta'addaci, ya kuma nemi hukumomin tsaro akan su kara zage dantsen su wajen damukar duk wadanda ke da hannu wajen aiwatar da munanan hare-hare a fadin kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel