Sauya sheka: Dukkanin nade-nade masu maiko Katsina da Lagas aka kai - Saraki

Sauya sheka: Dukkanin nade-nade masu maiko Katsina da Lagas aka kai - Saraki

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a ranar Talata ya hadu da magoya bayansa a Ilorin, inda anan ya fada masu cewa ya bar jam’iyyar All Progressives Congress saboda jajircewarsu akan ya aikata hakan da kuma shige masa gaba da Allah yayi.

Ya ci gaba da zargin cewa an nuna wariya ga jihar Kwara wajen nade-naden da gwamnatin APC ke yi.

Saraki yayi Magana ga manema labarai a Ilorin bayan ya halarci wata ganawa da gwamna da dukkanin mamabobin majalisar dokokin jihar, mambobin majalisar jihar 23 da kuma shugabannin kananan hukumomin jihar.

Sauya sheka: Dukkanin nade-nade masu maiko Katsina da Lagas aka kai - Saraki

Sauya sheka: Dukkanin nade-nade masu maiko Katsina da Lagas aka kai - Saraki

“Gwamnatin tarayya ta nada sama da mutane 200 mukamai masu maiko ba tare da ta ni ko kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara kowani gurbi na kawo wani ba. Komai ya tafi Katsina da Lagas. Ba don soyayyar da nake yiwa Naajeriya ba, dam un tarwatsa komai. Basu son mu a jam’iyyarsu. Basu son mu yan Kwara.” Inji Saraki.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Ina ma ace ban taba kasancewa dan APC ba – Kakakin majalisar Kwara ya jagoranci yan majalisa 23 zuwa PDP

A halin da ake ciki kakakin majalisar dokokin jihar Kwara, Dr. Ali Ahmed ya jagoranci mambobin majalisa 23 wajen sauya sheka daga APC zuwa PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel