Da dumi-dumi: Kaakakin jam'iyyar APC, Bolaji Abdullahi, ya fita daga APC

Da dumi-dumi: Kaakakin jam'iyyar APC, Bolaji Abdullahi, ya fita daga APC

Bayan kishin-kishin da fito ya karyata rahoton da ya bazama jiya bayan sauya shekan shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, daga APC, kaakakin jam'iyyar All Progressives Congress, Mallam Bolaji Abdullahi ya fita daga jam'iyyar yanzu.

Mallam Bolaji Abdullahi ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya saki da ranan nan ta shafin ra'ayi da sada zumuntarsa na Tuwita inda yace:

"Na bautawa jam'iyyar APC da tsoron Allah kuma da iyakan kokarina. kuma da na tsaya takara kuma na samu nasara a zaben taron gangamin da ya gabata, na yi hakan ne domin son cigaba da aikina."

Amma yayinda wasu ke shakkan kasancewana mai son jam'iyyar; abokan aikina na kokarin cin mutuncin ofishina, kuma an daina daukan shawarana saboda abokan siyasa na, ya zama wajibi in canza matsaya."

"Saboda haka, bisa ga abubuwan da ke faruwa a kasar da jam'iyyar, na yanke shawaran murabus daga kujerana na matsayin kaakakin jam'iyyar All Progressives congress APC."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel