Obasanjo ya ziyarci asibiti har an duba lafiyarsa

Obasanjo ya ziyarci asibiti har an duba lafiyarsa

- An duba lafiyar kwakwalwar, ido da sauran sassan jikin Obasanjo

- An duba lafiyar tasa ne a wani sabon asibitin da aka bude a jihar Bayelsa

Tsohon shugaban kasar nan Olusegun Obasanjo ya ziyarci cibiyar gwaje-gwaje da aka bude a jihar Bayelsa inda ya jinjinawa gwamnan jihar Seriake Dickson wajen samar da wuri mai cike da kayan aiki nagartattu.

Obasanjo ya ziyarci asibiti har an duba lafiyarsa

Obasanjo ya ziyarci asibiti har an duba lafiyarsa

Tsohon Shugaban ya kai wannan ziyara ne domin cika alkawrin da ya dauka tun a watan Fabrairun shekarar nan cewa da zarar gwamnatin ta bude cibiyar zai je domin yi masa gwaji.

Jim kadan bayan masa gwaje-gwaje wanda ya hada da gwajin hawan jini, ciwon hanta da sauransu, Obasanjo yace an kawo matakin da yan kasa ba sai sun fita kasashen waje ba domin bincikar lafiyarsu ba.

KU KARANTA: Dambarwar siyasa: An yiwa Tinubu, Oshiomhole da Amaechi wankin babban bargo

Ya ce "Duk abinda kake nema a kasashen duniya shi ne a Bayelsa, dan haka ban ga amfani fita waje neman magani ba, duba da irin wannan dama da muka samu, kawai mu yi amfani da ita".

"Lokacin da na kawo ziyara a watan Fabrairu naga kayan aiki masu nagarta wanda yan Najeriya zasu amfana dasu. Don haka ban ga amfanin zuwa kasashe irin su Dubai, tarayyar turai ko kuma kasar Amurka da sunan neman lafiya ba".

"An duba lafiyata kamar yadda duk inda naje a duniya za'ai min. An duba min ido, baki da kuma kwakwalwata, wanda daga bisani aka nuna min yadda suke".

"Bayan dana duba hoton kwakwalwar tawa sai na tambayi likita karin bayani akan ko lafiya take, ya bayyana komai lafiya yake game da kwakwalwata. Kuma abin burgewa shi ne kudin da zaka biya domin yi maka gwaji bai taka kara ya karya ba".

Bayan gama gwajin nasa a cibiyar gwaje-gwaje ta asibitin kwararru na jihar, Obasanjo ya zarce dakin taro na D.S.P. Alamieyeseigha domin halartar taro akan Abinda ya shafi mutuwar yara a yayin haihuwa.

Jim kadan bayan tarbarsa da gwamnan jihar Seriake Dickson, ya bayyana cewa ya kamata a wayar da kan jama'a game da mutuwar yara da mata a yayin haihuwa.

Bayan kamalla bayaninsa, gwamnan ya kara da cewa, gwamnatin tasa ta gina wata cibiya, inda za a ake tantance jabun magani domin ceto rayuwar al'umma.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel