Bayan Saraki akwai manyan yan siyasa daga APC da dama da za su dawo PDP - Wike

Bayan Saraki akwai manyan yan siyasa daga APC da dama da za su dawo PDP - Wike

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike, ya taya shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed murnar karfin gwiwar da suka tattara wajen sauya sheka zuwa PDP duk da barazana da tozarci da gwamnatin APC tayi masu.

Gwamna Wike ya ci gaba da kaddamar da cewa tozarci da barazana da gwamnatin APC ta dauko shine ya sa shugabannin PDP a fadin kasa suka jajirce domin tsayawa kan kafarsu wajen adawa da gwamnatin gajiyayyu.

Bayan Saraki akwai manyan yan siyasa daga APC da dama da za su dawo PDP - Wike

Bayan Saraki akwai manyan yan siyasa daga APC da dama da za su dawo PDP - Wike

Da yake jawabi ga manema labarai kan sauya shekar Saraki da gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed a ranar Talata a gidan gwamnatin Port Harcourt, Gwamna Wike yace matakin da hukunci ya kai a karkashin gwamnatin APC ya fi wadda aka gani a karkashin mulkin soja.

“Gwamnoni da manyan yan siyasa da dama za su kuma sauya sheka a kwanaki masu zuwa.” Inji gwamnan.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu shugaban PDP na Kwara ya sauya sheka zuwa APC, ya ce ba zai iya aiki da Saraki ba

Ya bayyana cewa babu amfanin ci gaba da irin wannan shugabanci wacce ta yasar da alkawaran da ta daukarwa mutanenta. Ya bayyana cewa PDP na da tanadi na makoma mai kyau ga Najeriya da kasar anan gaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel