Ba zan sauya sheka daga APC ba – Mataimakin kakakin majalisa

Ba zan sauya sheka daga APC ba – Mataimakin kakakin majalisa

Mataimakin kakakin majalisar wakilai Lasun Yussuff ya sake bayyana jajaircewarsa ga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), cewa ba zai taba barin jam’iyya mai mulki ba.

Yussuff wanda ya fadi a kudirinsa na son mallakar tikitin APC don takarar gwamna a jihar Osun a zabn da za’a yi a ranar 22 ga watan Satumba, ya nuna rashin gamsuwa da sakamakon zaben fid da gwani amma yace ba zai kalubalanci lamarin ba.

Ba zan sauya sheka daga APC ba – Mataimakin kakakin majalisa

Ba zan sauya sheka daga APC ba – Mataimakin kakakin majalisa

Da yake Magana a wani shiri karawa juna sani da hukumar Human and Environmental Development Agenda (HEDA) ta shiryawa mambobi da ma’aikatan kwamitin yakar laifuka na majalisar wakilai a Abuja, Yussuff ya kuma yi Allah wadai da yunkurin tsige gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom da mambobin majalisar dokokin jihar suka yi.

KU KARANTA KUMA: Ni na dakatar da rantsar da sabon mataimakin gwamna - Okorocha

Mataimakin kakakin majalisar ya kuma ce ba zai sanya hannunsa cikin kowani aiki da ya sabama jam’iyya ba amma ba zai hana masu yi ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel