Zargin barazana ga rayuwarsa: An tsaurara matakan tsaro kewaye da mataimakin gwamnan Kano

Zargin barazana ga rayuwarsa: An tsaurara matakan tsaro kewaye da mataimakin gwamnan Kano

Hukumomin yan sanda a Kano sun tsaurara tsaro kewaye da mataimakin gwamnan jihar, Farfesa Hafiz Abubakar, sakamakon wani korafi na cewa ana barazana ga rayuwarsa.

Kakakin yan sandan jihar, Magaji Musa Majia ya fadama jaridar Daily Trust cewa an dauki duk matakan da ya kamata domin kare rayuwar mataimakin gwamnan.

Jami’in hulda da jama’a na hedkwatar Zone One na Kano, DSP Muhammad Sambo Sokoto, ya ce ofishin mataimakin inspekto janar na yan sanda na kan korafin.

Zargin barazana ga rayuwarsa: An tsaurara matakan tsaro kewaye da mataimakin gwamnan Kano

Zargin barazana ga rayuwarsa: An tsaurara matakan tsaro kewaye da mataimakin gwamnan Kano

Mataimakin gwamnan ya aika takarda ga yan sanda da jami’an tsaro na jiha kan zargin barazana da ake yiwa rayuwarsa da shirye-shiryen tsige shi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu shugaban PDP na Kwara ya sauya sheka zuwa APC, ya ce ba zai iya aiki da Saraki ba

Abubakar, wani hadimin sanata Rabiu Musa Kwankwaso a korafinsa yayi zargin cewa gwamnatin jihar ta saki kudade don hada matasa daga kananan hokumomi 44 na jihar domin suyi zanga-zanga akan ci gaba da kasancewarsa a ofis.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel