Yanzu Yanzu shugaban PDP na Kwara ya sauya sheka zuwa APC, ya ce ba zai iya aiki da Saraki ba

Yanzu Yanzu shugaban PDP na Kwara ya sauya sheka zuwa APC, ya ce ba zai iya aiki da Saraki ba

Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party a jihar Kwara, Iyiola Oyedepo, yace lallai shi ba zai iya aiki tare da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ba don haka ya sanar da sauya shekarsa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress.

Oyedepo ya bayyana hakan a wayan tarho yayin wani shirin radiyo a Ilorin.

Ya bayyana cewa a yanzu haka yana Abuja domin mika takardansa na ajiye aiki a sakatariyar PDP.

Yanzu Yanzu shugaban PDP na Kwara ya sauya sheka zuwa APC, ya ce ba zai iya aiki da Saraki ba

Yanzu Yanzu shugaban PDP na Kwara ya sauya sheka zuwa APC, ya ce ba zai iya aiki da Saraki ba

Lauretta Onochie, hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari a shafukan zumunta ta maida martani ga ficewar shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki daga jam’iyyar All Progressive Congress, APC, zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

KU KARANTA KUMA: Bayan barin APC, Saraki na shirya makarkashiya don ci gaba da kasancewa shugaban majalisar dattawa

Da take martani Onochie ta bayyana cewa Saraki ya koma cikin amansa dumu-dumu. Ya sauya sheka zuwa PDP. Gwamnan jihar Kwara Fatai ma ya bi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel