Ni na dakatar da rantsar da sabon mataimakin gwamna - Okorocha

Ni na dakatar da rantsar da sabon mataimakin gwamna - Okorocha

Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo yayi ikirarin cewa shi ke da alhakin dakatar da ratsar da sabon mataimakin gwamnan jihar, Sir Calistus Ekenze a ranar Talata.

A cewar gwamnan, an dakatar da ratsarwar ne bayan umurnin da ya ba babban alkalin jihar domin biyayya ga umurnin kotu da ta dakatar da shi daga aikata hakan.

Gwamna Okorocha, wadda ya bayar da bayanin yace kafin ratsarwar, dakin taron da aka shirya gudanar da rantsarwan ya cika da baki, ciki hanrda manyan jami’an gwamnatin da shugabannin APC a jihar, kafin ya bayar da umurnin wadda ya fito ta hannun babban alkalin jihar, Barr. M.O. Nlemedim, domin dakatar da shirin.

Ni na dakatar da rantsar da sabon mataimakin gwamna - Okorocha

Ni na dakatar da rantsar da sabon mataimakin gwamna - Okorocha

Gwamnan ya bayar da bayanan ta hannun babban sakataren labaransa, Sam Onwuemeodo.

KU KARANTA KUMA: Saraki ya koma cikin amansa dumu-dumu – Lauretta Onochie

Yace ya zama dole a bi umurnin kotu ba tare da la’akari da wasu lamura da babban lauyoyin gwamnatin suka gabatar akan lamarin ba, tare da cewa ya zama dole gwamnatin ta bi umurnin kotu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel