Sanata Adamu ya bukaci Saraki ya furta cin amanar da ya yiwa Shugaba Buhari

Sanata Adamu ya bukaci Saraki ya furta cin amanar da ya yiwa Shugaba Buhari

A ranar Litinin din da ta gabata ne Sanata mai wakilcin jihar Nasarawa ta Yamma, Abdullahi Adamu, ya bukaci shugaban majalisar Dattawa Abubakar Bukola Saraki, akan ya gaggauta bayyana cin amana ta siyasa da ya yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Sanata Adamu ya nemi shugaban majalisar akan ya furta irin zagon kasa da rika yiwa shugaba Buhari musamman a lokutan da yake jinya ta neman lafiyar sa a Birnin Landan.

Sanatan ya bayyana hakan ne yayin mayar da martani dangane da kazafin da Saraki yake a gare sa, da cewar yana goyon bayan shugaba Buhari ne kadai domin samun kariyar sa sakamakon takaddamar dake tsakanin sa da hukumar hana yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC.

Sanata Adamu ya buƙaci Saraki ya furta cin amanar da ya yiwa Shugaba Buhari

Sanata Adamu ya buƙaci Saraki ya furta cin amanar da ya yiwa Shugaba Buhari

Sai dai a yayin ganawa da manema labarai na jaridar Vanguard, Mista Adamu ya bayyana cewa ba bu takaddama tsakanin sa da kowace kotu a kasar nan inda ya nemi Saraki akan ya bincika domin tabbatar da gaskiyar kalaman sa.

KARANTA KUMA: Ma su sababba rashin hadin kai da rikici za su kunyata - Fadar Shugaban 'Kasa

A cewar Sanata, shugaban majalisar ta su ya shirga karye ne kurum da shacin fadin sakamakon takaddamar sa da hukumar ta EFCC da tuni aka rufe babin ta tare da kaiwa karshen ta tun a ranar 28 ga watan Yunin 2015.

Mista Adamu wanda shine shugaban kwamitin kula da harkokin noma da kuma raya karkara na majalisar dattawa, ya zargi Saraki da kulla tuggun maye gurbin shugaba Buhari yayin da ya fita neman lafiya a shekarar 2017 da ta gabata.

Sanatan ya yi zargin cewa Saraki ne ya kulla tuggun tabarbarewar al'amurra a kasar nan domin maye gurbin shugaba Buhari da a tunanin sa ba zai dawo kasar nan ba, inda ya yi rashin sa'a manufar sa ba ta tabbata ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel