Bayan barin APC, Saraki na shirya makarkashiya don ci gaba da kasancewa shugaban majalisar dattawa

Bayan barin APC, Saraki na shirya makarkashiya don ci gaba da kasancewa shugaban majalisar dattawa

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki na shirya makarkashiyar ci gaba da kasancewa akan mulki duk da sauya shekarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), jaridar Premium Times ta rahoto.

Saraki a ranar Talata ya sanar da sauya shekarsa daga jam’iyya mulki yan makonni bayan ana ta rade-radin cewa zai aikata hakan.

Daga baya ya sanar da komawarsa PDP, jam’iyyar da ya bari a Janairu 2014 bayan ya zargi jam’iyyar da lalata damokradiyya.

Saraki, wadda ya kasance tsohon gwamnan jihar Kwara, ya zamo shugaban majalisar dattawa a 2015 bayan nasarar da APC ta yi a zabe. Shi da wasu sanatoci 10 sun koma jam’iyyar a Janairu 2014 bayan sun bar PDP.

Bayan barin APC, Saraki na shirya makarkashiya don ci gaba da kasancewa shugaban majalisar dattawa

Bayan barin APC, Saraki na shirya makarkashiya don ci gaba da kasancewa shugaban majalisar dattawa

Wani hadimin Saraki ya bayyana a ranar Talata cewa zai ci gaba da kasancewa a matsayinsa, tare da ba da misalai.

A cewar hadimin, duk da cewar za’a san masu rinjaye tsakanin APC da PDP bayan an dawo majalisa a watan Satumba, sashi na 50 na kundin tsarin mulkin 1999 bai hana dan majalisar tsiraru zamowa shugaban majalisar dattawan ba.

An fara samu baraka a jam'iyyar APC ne tun ranar Talatan da ya gabata, 24 ga watan Yuli, 2018 inda yan majalisan dattawa akalla 15 suka fita daga jam'iyyar APC da yan majalisan wakilar 35.

KU KARANTA KUMA: Saraki ya koma cikin amansa dumu-dumu – Lauretta Onochie

Abin mamakin shine Kaakakin majalisan wakilai, Yakubu Dogara da shugaban majalisan, Bukola Saraki, sun zauna a jam'iyyar. Masu sharhi sun bayyana cewa akwai wani kaidi da suke shirin kullawa da wannan rashin fita da sukayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel