Saraki ya koma cikin amansa dumu-dumu – Lauretta Onochie

Saraki ya koma cikin amansa dumu-dumu – Lauretta Onochie

Lauretta Onochie, hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari a shafukan zumunta ta maida martani ga ficewar shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki daga jam’iyyar All Progressive Congress, APC, zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP.

Da take martani Onochie ta bayyana cewa Saraki ya koma cikin amansa dumu-dumu. Ya sauya sheka zuwa PDP. Gwamnan jihar Kwara Fatai ma ya bi.

Hadimar shugaban kasar ta wallafa hakan ne a shainta na twitter bayan sahugaban majalisar dattawan ya sanar da sauya shekar sa zuwa PDP.

An fara samu baraka a jam'iyyar APC ne tun ranar Talatan da ya gabata, 24 ga watan Yuli, 2018 inda yan majalisan dattawa akalla 15 suka fita daga jam'iyyar APC da yan majalisan wakilar 35.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Bukola Saraki ya fita daga APC

Abin mamakin shine Kaakakin majalisan wakilai, Yakubu Dogara da shugaban majalisan, Bukola Saraki, sun zauna a jam'iyyar. Masu sharhi sun bayyana cewa akwai wani kaidi da suke shirin kullawa da wannan rashin fita da sukayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel