Manyan 'Yan siyasar da su ka tattara ina-su-ina-su su ka bar APC

Manyan 'Yan siyasar da su ka tattara ina-su-ina-su su ka bar APC

Kun ji labari cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Magoya bayan sa sun sauya-sheka daga APC. Mun kawo maku jerin wasu manyan ‘Yan siyasan da ake ji da su a kasar nan da yanzu su ka koma PDP.

Manyan 'Yan siyasar da su ka tattara ina-su-ina-su su ka bar APC

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya tsere daga APC

Ga jerin nan kamar haka:

1. Bukola Saraki

Ku na da labari cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya bar Jam’iyyar APC ya koma Jam’iyyar sa ta asali watau PDP. Saraki da dubban Mabiyan sa sun koma PDP ne bayan yace za a a APC ba za ta yiwu ba.

KU KARANTA: Dalilin da ya sa na bar APC – Inji Gwamnan Benuwai

2. Abdulfatahi Ahmad

Gwamnan Jihar Kwara Abdulfatahi Ahmad ya tattara ya bar APC inda ya koma Jam’iyyar adawa ta PDP. Gwamna Ahmad ya bi Mai gidan sa a siyasa watau Bukola Saraki wanda shi ma ya sanar da ficewar sa daga APC.

3. Ahmad Musa Ibeto

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Neja Ahmad Musa Ibeto ya fice daga APC ya koma PDP a makon nan. Ibeto wanda Gwamnatin Buhari ta aika Jakadanci zuwa Kasar Afrika ta Kudu ya ajiye aikin ya fara neman Gwamna.

Dama dazu kun ji cewa wani Dan ganin-kashe nin Saraki wanda shi ne Kakakin Jam’iyyar APC yace bai bar Jam’iyyar ta APC ba tukuna. Mai magana da yawun bakin na APC yace bai koma PDP ba kamar yadda ake rade-radi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel