Nagode da aka zabe ni in maye gurbin Gnassingbe inji Shugaba Buhari

Nagode da aka zabe ni in maye gurbin Gnassingbe inji Shugaba Buhari

- Buhari ya canji Shugaban Togo Faure Gnassingbe a matsayin Shugaban ECOWAS

- Shugaban na Najeriya yayi alkawarin yin bakin kokarin sa domin cigaba a Yankin

- Buhari ya nuna cewa bai son kujerar amma aka matsa masa dole ya hakura ya karba

Nagode da aka zabe ni in maye gurbin Gnassingbe inji Shugaba Buhari

Muhammadu Buhari ya zama sabon Shugaban Kungiyar ECOWAS

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya fito yayi magana bayan nada shi da aka yi a matsayin Shugaban Kungiyar ECOWAS ta Yankin Yammacin Nahiyar Afrika a wani taro da aka yi cikin makon nan a Kasar Togo.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa ya mika kan sa a kasa da ya ji cewa an nada sa Shugaban Kungiyar ta ECOWAS. Shugaban na Najeriya yayi alkawarin yin bakin kokari domin sauke wannan nauyi mai girma da aka daura masa.

Shugaban Najeriya Buhari ya bayyana cewa zai yi aiki da sauran Shugabannin Kasashen Afrika ta Yamma da kuma Gwamnatin babban Kungiyar ta ECOWAS wajen ganin an samu zaman lafiya da cigaba a fadin Yankin Afrika.

KU KARANTA: Za mu yi maganin masu tada kashe-kashe a Najeriya - Buhari

Dama tun kafin taron ya kankama, Shugaba Buhari ya bayyana cewa zaman lafiya da kuma ingantaccen mulki da shugabanci ne a gaban su. Kungiyar ECOWAS na cigaba da kokarin ganin an wanzar da zaman lafiya a Nahiyar.

Shugaban kasar yayi kokarin kin karbar wannan nauyi amma dai Shugabannin kasashen na ECOWAS su ka ga cewa shi ne ya fi kowa dacewa ya hau wannan kujera. Shugaba Buhari zai kira wani taro a kasar sa a Disamban bana.

Kun ji cewa Femi Gbajabiamila yayi kira ga Takwarorin sa na Jam’iyyar PDP da su hakura da hutun da su ka tafi kwanan nan su dawo Majalisa a maimakon tsayawa da su kayi ba su aikin komai sai sukar Shugaban kasa Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel