Akwai bukatar mu dawo bakin aiki saboda kasafin kudin bana – Gbajiabiamila

Akwai bukatar mu dawo bakin aiki saboda kasafin kudin bana – Gbajiabiamila

- Femi Gbajiabiamila ya nemi ‘Yan Majalisa su katse hutun su domin su dawo aiki

- Shugaban masu rinjayen yana kira Majalisar ta amince da rokon Shugaban kasa

- Gbajiabiamila yace akwai bukatar a zauna game da karashen kasafin kudin bana

Akwai bukatar mu dawo bakin aiki saboda kasafin kudin bana – Gbajiabiamila

‘Dan Majalisar Wakilan Tarayya ya nemi a dawo aiki a Najeriya

‘Yan Majalisar da ke karkashin Jam’iyyar APC mai mulki sun nemi ‘Yan uwan su su dawo bakin aiki. Shugaban masu rinjaye a Majalisar Honarabul Femi Gbajabiamila ne yayi wannan kira jiya a babban Birnin Tarayya na Abuja.

Femi Gbajabiamila yayi kira ga Takwarorin sa na Jam’iyyar PDP da su hakura da hutun da su ka tafi kwanan nan su dawo Majalisa a maimakon tsayawa da su kayi ba su aikin komai sai sukar Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA: APC ta dauki matakan ladabtar da shugaban majalisar dattawa

Hon. Gbajabiamila ya kuma yi magana game da rikicin siyasar da ke faruwa a Majalisar dokokin Jihar Benuwai inda ‘Yan APC da ba su fi a kirga a Majalisa ba su kayi kokarin tsige Gwamna. Femi Gbajabiamila yace hakan ba za ta sabu ba.

‘Dan Majalisar ya nuna cewa yunkurin da ake yi a Benuwai na tsige Gwamna Samuel Ortom ba zai kai ko ina ba sannan kuma yace bau kamata a ga hannun Shugaban kasa Buhari a cikin wannan rikici da ya shafi wata Jiha mai gashin kan-ta.

Gbajabiamila yace bai ga dalilin da zai sa Jam’iyyar PDP ta rika kokarin hana Majalisa ta zauna domin ganin an amince da ragowar kasafin kudin wannan shekara ba. ‘Dan Majalisar yace idan ta kama ‘Yan APC kadai sun isa su kira zama.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel