Zaben 2019: Fitar Saraki ba za ta hana mu nasara ba – Inji Gwamna Okorocha

Zaben 2019: Fitar Saraki ba za ta hana mu nasara ba – Inji Gwamna Okorocha

A jiya labari ya zo mana cewa Shugaban Gwamnonin Jam’iyyar APC mai mulki watau Rochas Okorocha ya fito ya bayyana cewa ko babu Shugaban Majalisa Bukola Saraki a APC za su ci zabe mai zuwa a 2019.

Zaben 2019: Fitar Saraki ba za ta hana mu nasara ba – Inji Gwamna Okorocha

Gwamna Okorocha ya fadawa Saraki Allah raka taki gona

A jiya Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki ya fice daga APC ya koma PDP. Gwamnan Imo Rochas Okorocha yayi magana bayan jin wannan labari inda ya bayyana cewa sauyin shekar ba za ta canza komai ba.

Gwamnan yake cewa Shugaban Majalisar yana da damar shiga duk Jam’iyyar da ya ga dama. Okorocha yace Jam’iyya tamkar mota ce da aka hawa domin a isa inda ake nufi. Inda yace idan Saraki bai gamsu a APC ba sai ya bi wata.

KU KARANTA: Da in koma PDP gara in hakura da siyasa - Uzor Kalu

Rochas Okorocha yayi addu’a Allah ya ba Bukola Saraki sa’a amma fa yace ko da shi, ko babu shi dama za su lashe zaben 2019. Gwamnan yace yayin da Saraki su ka tsere, wasu kuma neman shigowa cikin Jam’iyyar APC su ke yi.

Shi kuma Atiku Abubakar ya ji dadin sauya-shekan da Saraki yayi, Atiku yana cewa yadda APC tayi wa Shugaban Majalisar Kasar Bukola Saraki, haka tayi wa Najeriya. Atiku yace Jam'iyyar APC ta kashe tattalin arzikin Najeriya.

Gwamna Rochas Okorocha duk ya bayyana wannan ne lokacin da ya zanta da manema labarai bayan yayi wani kus-kus da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole a jiya Ranar Talata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel