2019: Jama’a sun yi ta kai-komo bayan jin Saraki ya koma PDP

2019: Jama’a sun yi ta kai-komo bayan jin Saraki ya koma PDP

Kun ji labari cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya tsere daga Jam’iyyar APC mai mulki jiya ya koma PDP. Saraki ya koka da irin abubuwan da su ka faru a Gwamnatin APC wanda yace su ka sa ya sauya-sheka.

2019: Jama’a sun yi ta kai-komo bayan jin Saraki ya koma PDP

Shugaban Majalisar kasar nan Saraki ya koma Jam'iyyar PDP

Jama’a da dama dai su na ta tofa albarkacin bakin su bayan da su ka ji cewa Bukola Saraki ya koma Jam’iyyar da ya fito. Wasu sun ji dadin wannan labari yayin da wasu kuma su kace abin yayi masu dadi kwarai da gaske.

Salihu Abubakar Salihu yana cewa:

“Allah raka taka gona, mu dai mu na tare da Buhari. Manyan kasar nan duk su na kokarin barin Buhari a yakin da ya ke yi, ko don wannan, dole mu rike Shugaba Buhari.”

Shi kuwa Jubril Gawat wanda yayi fice a shafin sadarwa na zamani na Tuwita cewa yayi:

“Addu’a ta Jam’iyyar PDP ta tsaida Bukola Saraki a matsayin ‘Dan takarar Shugaban kasar ta, domin su fafata da Shugaba Buhari”

A baya dai Mista Jubril Gawat ya nuna cewa Shugaban Majalisar Dattawan kasar Bukola Saraki ya ci amanar Jam’iyyar sa ta APC inda ya mika kujerar Mataimakin sa ga ‘Dan Jam’iyyar adawa watau Sanata Ike Ekweremadu.

Shi kuma Mu’awiyah Muye wanda yana cikin masu ba Gwamnan Jihar Neja shawara ya nuna cewa sai a fara shirin wanda zai maye gurbin Bolaji Abdullahi wanda yaron Bukola Saraki ne a Majalisar Jam’iyyar mai mulki.

Shi kuma tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar cewa yayi yadda APC tayi wa Shugaban Majalisar Kasar Bukola Saraki, haka tayi wa Najeriya. Atiku yace Jam'iyyar APC ta kashe tattalin arzikin Najeriya a mulkin ta.

Dan ganin-kashe nin Saraki wanda shi ne Kakakin Jam’iyyar APC yace bai bar Jam’iyyar ta APC ba tukuna. Mai magana da yawun bakin na APC yace bai koma PDP ba kamar yadda ake rade-radi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel