Almundahana: Sai fa ka amsa tuhumar EFCC – Kotu ta fadawa tsohon gwamnan PDP

Almundahana: Sai fa ka amsa tuhumar EFCC – Kotu ta fadawa tsohon gwamnan PDP

A yau, Talata, wata babbar kotu dake Legas tayi watsi da matakin da tsohon gwamnan jihar Abiya, Orji Uzor Kalu, ya dauka na shaida mata cewar ba bu tuhumar da zai amsa daga zargin almundahanar da ake yi masa.

Hukumar yaki da yiwa tattalin arziki ta’annati (EFCC) ce ta gurfanar da Kalu tare da wani kamfaninsa bisa zargin karkatar da kudin jihar Abiya, biliyan N2.9bn, lokacin da yake gwamna daga 1999 zuwa 2007.

Kalu ya kafe kan cewar bai aikata ko daya daga cikin laifukan da ake tuhumarsa da su ba, a saboda haka babu wata tuhuma da zai amsa dangane da batun zargin shi da almundahana, Lamarin ya jawo tsaiko a shari’ar.

Almundahana: Sai fa ka amsa tuhumar EFCC – Kotu ta fadawa tsohon gwamnan PDP
Orji Kalu

Hakan ya saka a kwanakin baya shugabar kotun daukaka kara, Zainab Bulkachuwa, ta bayar da umarnin a yankewa tsohon gwamnan jihar Abiya, Orji Kalu, hukunci kafin karshen watan Satumba na shekarar nan, 2018.

Jastis Mohammed Idris, alkalin kotun da aka gurfanar da Orji Kalu, ya sanar da hakan yayin da kotun ta zauna yau domin cigaba da sauraron karar a Legas.

DUBA WANNA: Wanke Bafarawa: Kada ma ka dauka ka ci bulus - EFCC ta fadawa Bafarawa

Farfesa Awa Kalu, lauyan dake kare Kalu ne ya rubuta takardar neman Bulkachuwa ta bawa Jastis Idris dammar cigaba da sauraron karar da aka dade ana fafatawa.

Lauyan ya mika wannan bukata ne ga Bulkachuwa bisa dogaro da sashe na 396(7) da ya bawa alkalin da aka yiwa karin girma damar karasa dukkan shari’ar dake hannunsa kafin a yi masa karin girman.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel