Ina maraba da ficewar Bukola Saraki daga APC, dawo gida- Atiku Abubakar

Ina maraba da ficewar Bukola Saraki daga APC, dawo gida- Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana farin cikinsa da wani babbar rashi da jam’iyya mai mulki, jam’iyyar APC ta yi a sakamakon ficewar shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki daga cikinta.

Atiku ya bayyana haka ne a shafinsa na Tuwita, kamar yadda Legit.ng ta gano, inda yace; “Na ji dadin samun labarin ficewar shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki daga APC.”

KU KARNTA: Likafa ta cigaba: Shugaba Buhari ya zama shugaban kungiyar kasashen yammacin Afirka

Ina maraba da ficewar Bukola Saraki daga APC, dawo gida- Atiku Abubakar

Saraki da Atiku Abubakar

Sai dai Atikun ya danganta abubuwan da jam’iyyar ta yi masa da abuuwan da suka yi ma Najeriya, inda yace jam’iyyar APC ta gurgunta dimukradiyyan Najeriya, kamar yadda ta gurgunta tattalin arzikin Najeriya.

Legit.ng ta ruwaito Atiku yana shawartar Sanata Bukola Saraki da ya shiga jam’iyyar dake da burin taimaka ma yan Najeriya, tare da tabbatar da ingantaccen tsarin Dimukradiyya a Najeriya, da kuma karfin tattalin arziki mai daurewa.

“Ina kira ga Sanata Saraki ya shigo jam’iyyar PDP, Allah ya yi ma Najeriya albarka, Allah ya yi ma jam’iyyar PDP Albarka.” Inji tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel