Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya caccaki gwamnatin shugaba Buhari

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya caccaki gwamnatin shugaba Buhari

Tsohon shugaban babban bankin tarayyar Najeriya kuma Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi ya caccakin gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Buhari da kasar Afrika ta kudu bisa kan kin rattaba hannu akan yarjejeniyar kasuwanci a Nahiyar Afrika.

Sarkin yace abun takaici ne ace kasashen Afrika 44 duka sun sanya hannu a takardar amma Najeriya da Afrika ta Kudu sun kekashe kasa sun kiya inda yace ya kamata a sake zama domin lalubo bakin zaren.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya caccaki gwamnatin shugaba Buhari

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya caccaki gwamnatin shugaba Buhari

KU KARANTA: Yan sandan Najeriya sun cafke mai buga kudin jabu

Legit.ng ta samu cewa Sarkin dai ya fadi hakan ne lokacin da yake jawabi a wajen taron kwararru a fannoni da dama na 'yan Najeriya mazauna kasashen waje.

A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayyar Najeriya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta shirya tsaf domin kafa sabbin ma'aikatu guda biyu a karkashin babbar ma'akatar dake kula da kimiyya da fasaha watau ministry of Science and Technology a turance.

Mai'aikatun da za'a kafa din dai sune na kwararowar hamada da zaizayar kasa da kuma bincike watau National Agency for Desertification & Erosion Research (NADER) a turance da kuma ta na'urorin zamani watau Research in Robotics & Artificial Intelligence (NARRAI) a turance.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel