Likafa ta cigaba: Shugaba Buhari ya zama shugaban kungiyar kasashen yammacin Afirka

Likafa ta cigaba: Shugaba Buhari ya zama shugaban kungiyar kasashen yammacin Afirka

Wani rahoto da muka samu ta tabbatar da cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zama sabon shugaban kungiyar kasashen nahiyar yammcin Afirka, ECOWA, a ranar Talata, 31 ga watan Yuli.

Hadimin Buhari akan kafafen watsa labaru na zamani, Bashir Ahmad ne ya bayyana haka a shafinsa na Tuwita, inda yace an sanar da Buhari a matsayin shugaban ECOWAS ne bayan wani taron sirri da shuwagabannin kasashen yammacin Afirka suke yi a birin Lome.

KU KARANTA: Adadin layukan wayoyin Salula a Najeriya sun kai miliyan 162.3

A ranar Litinin, 30 ga watan Yuli ne shugaba Buhari ya isa babban birnin ksar Togo, Lome don halartar taron kungiyar ECOWAS na musamman, inda ya smau rakiyar gwamnan jihar Kros Ribas, Ben Ayade, gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akerdolu da kuma ministan sadarwa, Shittu Adebayo.

Sauran manyan jami’an gwamnati da suka raka Buhari sun hada da gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello da ministan kudi, Uwargida Kemi Adeosun, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel