Gwamna Dickson ya yabawa Musulmai bisa tabbatar da zaman lafiya a jihar Bayelsa

Gwamna Dickson ya yabawa Musulmai bisa tabbatar da zaman lafiya a jihar Bayelsa

Wani rahoton mai cike da son barka da muka samu da sanadin shafin jaridar The Nation ya bayyana cewa, gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson, ya yabawa Musulmai bisa tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali cikin jihar sa.

Gwamna Dickson ya shawarci al'ummar Musulmi musamman mazauna Birnin Yenagoa akan su ci gaba da tabbatar da kiyaye dokoki domin inganta zaman lafiya da kuma kwanciyar hankalia zamantakewar su.

Kamar yadda kakakin gwamnatin jihar Francis Agbo ya bayyana cewa, gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da mambobin kungiyar al'amurran da suka shafi Musulmai ta ziyarci fadar sa a birnin Yenagoa.

Gwamna Dickson ya yabawa Musulmai bisa tabbatar da zaman lafiya a jihar Bayelsa

Gwamna Dickson ya yabawa Musulmai bisa tabbatar da zaman lafiya a jihar Bayelsa

Gwamnan ya ke cewa, har ila yau jihar Bayelsa gida ce ga dukkanin 'yan Najeriya ba tare da la'akari da bambance-bambancen addinai ko al'adun su ba.

Ya nemi al'ummar jihar akan su ci gaba da jajircewa tare da bayar da hadin kai ga hukumomin tsaro domin inganta tsaro, zaman lafiya gami da kwanciyar hankali.

KARANTA KUMA: Babban Ma'aikacin 'Karamar hukuma ya kashe kansa murus a jihar Ekiti

Dickson ya lura cewa, tun kafuwar gwamnatin sa babu wata babbar matsala ko tashin-tashina da ta hadar da Musulmai a jihar sa, inda ya nemi su kan kara zage dantsen su wajen ci gaba da tabbatuwar hakan a fadin jihar.

A yayin jawaban sa dangane da bukatar tallafawa maniyyata yayin sauke farali, gwamna Dickson ya bayyana cewa a halin yanzu gwamnatin sa ba ta da halin daukar wannan nauyi na bayar da wani tallafi ga Maniyyatan wajen sauke farali a kasa mai tsarki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel