Ofireshon Lafiya Dole: Manjo Janar Abba Dikko ya maye gurbin Rogers Nicholas

Ofireshon Lafiya Dole: Manjo Janar Abba Dikko ya maye gurbin Rogers Nicholas

A yau, Talata, ne Manjo Janar Abba Dikko ya karbi ragamar jagorancin rundunar dakarun soji ta Ofireshon Lafiya Dole dake aikin kakkabe ‘yan kungiyar Boko Haram da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Dikko ya karbi jagorancin rundunar ne daga hannun abokin aikinsa Manjo Janar Rogers Nicholas, wanda aka nada a watan Disamba na shekarar 2017. Nicholas ya mika jagoranci ga Dikko a wata cibiya dake sansanin soji a garin Maidugurin jihar Borno.

Nicholas ya yi kira ga sabon kwamandan day a dora a kan nasarorin da ya tarar an samu a kan mayakan kungiyar Boko Haram.

Ofireshon Lafiya Dole: Manjo Janar Abba Dikko ya maye gurbin Rogers Nicholas

Manjo Janar Abba Dikko ya maye gurbin Rogers Nicholas

Kazalika ya yi godiyar ga rundunar sojoji dake jihar Borno bisa goyon bayan da suka bas hi lokacin da yake jagorantar su.

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar rundunar soji dake aikin mayar da martani cikin gaggawa (Quick Response Force) tayi nasarar cafke wasu 'yan fashi da makami a Felele dake kan hanyar Lokoja zuwa Okene.

DUBA WANNAN: Kotu ta wanke tare da sallamar mabiya Shi'a 100 da gwamnati ta gurfanar

'Yan fashin sun yi basaja cikin kakin sojoji domin yaudarar matafiya su dauka jami'an tsaro ne.

Hukumar soji, ta bakin Texas Chukwu, darektan yada labarai, ta ce ta yi nasarar kama uku daga cikin 'yan fashin, Savior Denis - mai shekaru 39, Isaac Donald - mai shekaru 35, da kuma Joseph Isah - mai shekaru 35, yayin da daya daga cikinsu, Mista Arten ya rasa ransa yayin musayar wuta da dakarun soji.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel