Yanzu-yanzu: Bukola Saraki ya fita daga APC

Yanzu-yanzu: Bukola Saraki ya fita daga APC

Labarin da ke shigowa yanzu da dumi-dumi na nuna cewa bayan rikice-rikice, zanga-zanga da fadan baki, shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki, ya sanar da fitarsa daga jam'iyyar APC.

Shugaban majalisan ya yi wannan sanarwa ne da yammacin nan ta shafin sada ra'ayi da zumuntarsa na Tuwita.

A jawabin yace: " Ina son sanar da yan Najeriya cewa bayan shawarwarin da nayi sosai, na yanke shawaran fita daga jam'iyyar All Progressives Cogress APC."

Wannan abi na faruwa ne bayan wasu daruruwan matasa sun tafi zanga-zanga sakatariyan jam'iyyar APC da ke babban birnin tarayya Abuja.

An fara samu baraka a jam'iyyar APC ne tun ranar Talatan da ya gabata, 24 ga watan Yuli, 2018 inda yan majalisan dattawa akalla 15 suka fita daga jam'iyyar APC da yan majalisan wakilar 35.

Abin mamakin shine Kaakakin majalisan wakilai, Yakubu Dogara da shugaban majalisan, Bukola Saraki, sun zauna a jam'iyyar. Masu sharhi sun bayyana cewa akwai wani kaidi da suke shirin kullawa da wannan rashin fita da sukayi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel