Da dumi-dumi: Kotu ta wanke tare da sallamar mabiya Shi’a 100

Da dumi-dumi: Kotu ta wanke tare da sallamar mabiya Shi’a 100

A yau, Talata, ne babbar kotun Kaduna ta wanke tare da sallamar wasu mabiya Shi’a 100 daga cikin ‘yan kungiyar 200 da gwamnatin jihar ta gurfanar tun shekarar 2015 bisa zarginsu da tayar da tarzoma da haddasa husuma.

Wannan rahoto na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin kungiyar Shi’a, Ibrahim Musa, ya fitar a yau bayan hukuncin kotun.

A cewar jawabin nasa, “Wannan hukunci bai tsaya a matsayin nasara ga mabiya Shi’a ba, nasara ce a kan danniya da muzgunawa. Nasara ce adalci a kan zalunci da cin mutunci .”

Da dumi-dumi: Kotu ta wanke tare da sallamar mabiya Shi’a 100

Shugaban Shi'a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky

Gwamnatin jihar Kaduna ta gurfanar da mabiya Shi’a 200 a gaban kotu bayan wata afkuwar hatsaniya tsakaninsu da dakarun soji a watan Disamba na shekarar 2015.

DUBA WANNAN: Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai ya fada komar EFCC

Bayan hatsaniyar ne gwamnatin Najeriya ta kama shugaban mabiya Shi’a na Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, kuma har yanzu take cigaba da tsare shi.

Tun bayan kama shi ne magoya bayansa k eta gudanar da zanga-zanga a garuruwa daban-daban, musamman Kaduna da Abuja.

Magoya bayan Shi'ar sun nuna jin dadinsu bisa wannan hukunci na kotu tare da bayyana cewar ba zasu huta ba har sai gwamnati ta saki shugabansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel