Da duminsa: Mataimakin shugaban majalisar dattijai na can hannun matambayan hukmar EFCC

Da duminsa: Mataimakin shugaban majalisar dattijai na can hannun matambayan hukmar EFCC

Jaridar Premium Times ta wallafa rahoton cewar yanzu haka mataimakin shugaban majalisar dattijai, Ike Ekweremadu, na can tsare a ofishin hukumar yaki da yiwa tattalin arziki ta’annati (EFCC) tun safiyar yau.

Jaridar ta bayyana cewar majiyarta ta tabbatar mata da cewar Ekweremadu ya isa ofishin hukumar EFCC ne da misalign karfe 9-10 na safe kumar har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto yana can.

Wani jami’in hukumar ta EFCC, da jaridar Premium Times bat a ambaci sunansa ba, ya sanar da ita cewar Mista Ekweremadu na dakin amsa tambayoyi kamar yadda ta ce wani jami’in hukumar ya tabbatar mata.

Da duminsa: Mataimakin shugaban majalisar dattijai na can hannun matambayan hukmar EFCC

Ike Ekweremadu

Muna son ya amsa wasu tambayoyi ne masu alaka da almundahana da rashawa. Bamu san lokacin da zamu sake shi ba, ku dai jira zuwa yamma mu gani,” wani jami’in hukumar ya sahidawa Premium Times.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya dauki hankulan shugabanni a taron ECOWAS, kalli hotuna

A satin day a gabata ne hukmar EFCC ta aikewa Ekweremadu takardar gayyata amma ya yi burus da gayyatar, lamarin day a saka jami’an EFCC sun tsare kofar shiga gidansa dake rukunin gidajen ‘yan majalisu na Apo dake birnin tarayya, Abuja.

EFCC na tuhumar Ekweremadu da mallakar wasu kadarori a kasashen waje ba bisa ka’ida ba tare da wasu laifuka masu nasaba da cin hanci da rashawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel