Masu neman a tsige Saraki sun yi zanga-zanga a hedikwatar APC dake Abuja

Masu neman a tsige Saraki sun yi zanga-zanga a hedikwatar APC dake Abuja

Wasu mutane dake neman a tsige Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, sun yi zanga-zanga dauke da kwalayen rubuce-rubuce, a hedikwatar jam’iyyar APC da ke babban birnin tarayya Abuja.

Masu zanga-zangar da suka ce su mambobin APC ne daga jihar Kwara, sun kuma yaba da matakin da uwar jam’iyya ta dauka inda ta rushe shugabancin shugabannin APC na jihar Kwara.

Koda yake zuwa yanzu Saraki bai sanar da ficewar sa daga APC ba, ana kyautata zaton cewa nan ba da jimawa ba zai bayyana ficewar ta sa.

Masu neman a tsige Saraki sun yi zanga-zanga a hedikwatar APC dake Abuja

Masu neman a tsige Saraki sun yi zanga-zanga a hedikwatar APC dake Abuja

Sai dai kuma masu zanga-zangar sun ce ba za su tsaya sai sun jira har lokacin da Saraki ya fice daga APC a lokacin da ya ga dama ba.

KU KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Yadda shugaba Buhari ya dauki hankulan shugabanni a taron ECOWAS

Da ya ke yi wa manema labarai jawabi a harabar sakateriyar APC a yau Talata, Tayo Awodiji ya yi kira da a kori Saraki, saboda zagon-kasa da ya ke yi wa jam’iyyar APC.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Tsohon mataimakin gwamnan jihar Niger kuma jakadan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu, Alhaji Ahmed Ibeto, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar PDP a jihar.

Ibeto wadda ya kasance mataimakin gwamnan tsohon gwamnan jihar Niger Muazu Babangida Aliyu na tsawon shekaru takwas ya sauya sheka ne daga PDP zuwa APC a zaben 2014/2015 bayan ya fadi a zaben fid da gwani.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel