Jaraba: Yadda wasu matasa su 8 suka yi ma wata Akuya fyade yayin da take dauke da ciki

Jaraba: Yadda wasu matasa su 8 suka yi ma wata Akuya fyade yayin da take dauke da ciki

Rundunar Yansandan kasar India sun kaddamar da farautar wasu matasa su takwas da ake zargi da zakke ma wata Akuya mai dauke da juna biyu, ta hanyar yi mata fyade, wanda hakan yayi sanadin mutuwar Akuyar, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ana tuhumar matansan ne a karkashin sashi na 377 na kundin hukunta manyan laifuk, wanda ya haramta auren jinsi, ko kuma saduwa ba kamar yada ake yi bisa al’ada ba.

KU KARANTA: Rana bata karya: EFCC ta kaddamar da bincike akan Gwamna Fayose da Uwargidarsa

Bugu da kari yansanda na tuhumar matasan da cin zarafin dabba, wanda hakan yi ma dokar hana cin zarafin dabba karan tsaye ne.

“Mun gano guda uku daga cikinsu, kuma jami’an Yansandanmu suna farautarsu ruwa a jallo, muna sa ran zamu kama su nan bada jimawaba.” Inji kaakakin Yansandan yankin, Naazneen Bhasin.

Bhasin yace mai Akuyar ne ya kama uku daga cikin matasan turmi da tabarya yayin da suke yi ma Akuyar fyade da tsakar dare a satin daya gabata, ya kara da cewa bayan wani dan kankanin lokaci ne kuma Akuyar ta mutu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel