Rikicin Kwankwasiyya: An shirya biyan Mutane kudi su yi wa Kwankwaso zanga-zanga

Rikicin Kwankwasiyya: An shirya biyan Mutane kudi su yi wa Kwankwaso zanga-zanga

Gwamnatin Jihar Kano ta shirya biyan mutane su fito fili su yi zanga-zanga domin nuna cewa ba a tare da tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma Mataimakin Gwamna na yanzu Hafiz Abubakar.

Rikicin Kwankwasiyya: An shirya biyan Mutane kudi su yi wa Kwankwaso zanga-zanga

Ana zargin Ganduje ya fara shiryawa ‘Yan Kwankwasiya kulalliya

Gwamnatin Umar Abdullai Ganduje ta shirya biyan Jama’a kudi domin yin zangar-zangar da za ta nuna cewa ba a tare da ‘Yan Kwankwasiyya a Kano. Jiya da dare ne Gwamnan na Kano ya gama shirya wannan danyen aiki.

Labarin da mu ke ji shi ne Gwamna Ganduje ya zauna da Kwamishinan sa na Kananan Hukumomi watau Murtala Garo da kuma Shugaban Kungiyar Kananan Hukumomi na Jihar Lamin Sani domin kista wannan aiki a makon nan.

KU KARANTA: An tsige Mataimakin Gwamnan Imo a Majalisar dokoki

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rahoto cewa an shirya yadda za a biya mutane kudi su fito su yi Kwankwaso da Mataimakin Gwamnan Jihar bore sai kwatsam kuma aka samu canjin shugabanci a Majalisar dokokin Jihar ta Kano.

A yau ne aka shirya fara gudanar da zanga-zanga bayan an dibi kudi daga kowace Karamar Hukuma ta Jihar. Hakan dai bai yiwu ba bayan abin da ya faru jiya Jihar. Gwamnatin Kano dai tayi maza ta karyata wannan zargi.

Dama can mun fara jin kishin kishin din cewa Gwamnatin Jihar Kano ta sa 'Yan Sanda sun daure wasu Bayin Allah da su ka fito su ka kona tsintsiya kwanan nan domin nuna mubaya'ar su ga tsohon Gwamna Rabiu Kwankwaso.

Dazu kun ji cewa Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Hafiz Abubakar ya fadawa DSS cewa yana cikin babban hadari a halin yanzu. Ana tunani Gwamna Ganduje ya shiryawa Mataimakin na sa makarkashiyar a tsige sa a Majalisa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel