Rana bata karya: EFCC ta kaddamar da bincike akan Gwamna Fayose da Uwargidarsa

Rana bata karya: EFCC ta kaddamar da bincike akan Gwamna Fayose da Uwargidarsa

- Hukumar EFCC ta kaddamar da binciken kwakwaf akan Gwamna Fayose da Matarsa

- EFCC na tuhumar Fayose da dumbuzar kudaden al'ummar jihar Ekiti

Gwamnan jihar Ekiti ya shiga uku bayan da ingantattun rahotanni suka tabbatar da cewar hukumar yaki da rasha da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta kaddamar da bincike akansa da uwargidarsa Feyisetan, inji rahoton jaridar The Cables.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin wadanda EFCC ke bincika akwai wani hadiminsa, Toyin, kwamishinan kudi na jihar, Oluyemisi Owolabi, babban akanta na jihar da Kaakakin gwamnan, Lere Olayinka.

KU KARANTA: Zakarar da Allah ya nufa da cara: Wata yarinya ta tsere daga hannun mayakan Boko Haram

Rana bata karya: EFCC ta kaddamar da bincike akan Gwamna Fayose da Uwargidarsa

Gwamna Fayose da Uwargidarsa

Majiyar tamu ta ci karo da wasu wasiku dauke da kwanan wata 20 ga watan Yulin shekarar 2018, wanda EFCC ta aika ma babban manajan bankin Access, suna bukatar karin bayanai game da wasu asusun banki guda hudu dake dauke da sunan Ayodele Peter Fayose, da wasu asusun bankin guda biyar dauke da sunan Feyisetan Helen O Fayose.

Haka zalika hukumar ta aika ma wasu manyan bankunan kasar nan inda Fayose da hadimansa suke ajiyan kudade, a cikin wasikun, EFCC ta umarci jami’in bin doka da ka’ida na bankunan dasu gurfana gabanta a ranar Talata, 24 ga watan Yuli, kwanaki goma bayan faduwa zaben gwamna da dan takarar Ayo Fayose yayi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel