Atiku yace PDP za ta tafka babban kuskure idan har ta hana shi tikitin takarar shugaban kasa

Atiku yace PDP za ta tafka babban kuskure idan har ta hana shi tikitin takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa PDP za ta tafka mummunan kuskure matukar da hana shi tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019.

Atiku ya bayyana haka ne ya bakin Kaakakin kungiyar yakin neman zabensa, Segun Showunmi, wanda yace ya kamata yan Najeriya su goyi bayan Atiku Abubakar Wazirin Adamawa sakamakon kwarewarsa.

KU KARANTA: Zakarar da Allah ya nufa da cara: Wata yarinya ta tsere daga hannun mayakan Boko Haram

Atiku yace PDP za ta tafka babban kuskure idan har ta hana shi tikitin takarar shugaban kasa

Atiku

“Atiku ya banbanta da sauran yan siyasan Najeriya, musamman masu neman takarar shugaban kasa, dayawa daga cin yan takarkarunnan basa da jama’a face a yankunnan da suka fito, wasunsu suna neman takarar ne kawai don ace sun yi takara.

“Ba zasu iya bayyana maka manufofinsu ba, wannan yasa kasar Najeriya ke bukatar Atiku Abubakar, mutumin dake da kwarjini a duk Duniya gaba daya, Atiku yafi dukkanin yan takarar, duk cikinsu babu wanda zai iya karawa da Buhari a 2019 ya kai labari.

“Don haka akwai rashin dabara idan aka dauko wani daga PDP don ya kara da Buhari sabanin Atiku Abubakar, wannan zai zamo babban kuskure da PDP za ta tafka.” Inji shi.

Daga karshe Segun yace Atiku mutum ne mai sauraron ra’ayoyi daban daban tare da daukan shawarwari masu amfani, haka zalika yana tafiya da kowane irin mutum ba tare da nuna bambancin kabila ko addini ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel