Sufurin Jiragen Kasa: Burin mu gamsuwar al'umma ba neman riba ba - Amaechi

Sufurin Jiragen Kasa: Burin mu gamsuwar al'umma ba neman riba ba - Amaechi

Ministan sufuri, Mr Rotimi Amaechi yace burin shi shine titin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna ya daidaita a cikin shekarar, ba wai neman riba suke yi ba

Sufurin Jirgin Kasa: Burin mu gamsuwar al'umma ba neman riba ba - Amaechi

Sufurin Jirgin Kasa: Burin mu gamsuwar al'umma ba neman riba ba - Amaechi

Ministan sufuri, Mr Rotimi Amaechi yace burin shi shine titin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna ya daidaita a cikin shekarar, ba wai neman riba suke yi ba.

Amaechi yayi wannan maganar ne a wata tataunawa da yayi a Abuja, ranar Talatar nan, a bikin cika shekaru biyu dayin layin dogon.

Titin jirgin kasan ya fara aiki ne a ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2016, a matsayin shirin gwamnatin tarayya, karkashin hukumar sufuri ta Najeriya.

DUBA WANNAN: Dubun wasu 'yan fashi ta cika, yayinda sojoji suka yi sukuwar sallah a kansu

Ministan yace, ma'aikatan ta zuba taira miliyan 56 a duk wata kuma ana samun Naira miliyan 16 ne kafin a kara kudin.

"Munyi haka ne na shekara biyu, mataki na farko da na dauka, shine rage kudin, wanda da gangan nayi kuma daga baya mutane suka bukaci da mu kara. Inda muka kara zuwa yanda zasu iya biya.

"Mutane sun fi son jirgin kasan, saboda akwai arha kuma yafi kwanciyar hankali.

"Lokacin da muka fara, muna zuba Naira miliyan 56 duk wata ne, amma muna samun Naira miliyan 16 ne, saboda tallafin da muke yi.

"Mutane suna son jirgin kasan ne saboda muna aiki akan lokaci, ga tsafta kuma mun sa kudin da arha, mun nuna cewa zamu iya da kanmu, ba tare da taimakon turawa ba. NRC ce ta ke aikin," yace.

Manajan NRC, Mista Fidet Okhiria yace ba riba yake bukata ba, gamsuwar jama'a yake so.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel