Buhari zai gama aikin dogon jirgin kasan Warri kafin 2019 – Amaechi

Buhari zai gama aikin dogon jirgin kasan Warri kafin 2019 – Amaechi

Ministan sufuri na kasar nan watau Rotimi Amaechi ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta kusa kammala wani aikin jirgin kasa da ake yi a tsakiyar Arewa da kuma Kudancin Kasar nan tsakanin Itakepe har zuwa cikin Warri.

Buhari zai gama aikin dogon jirgin kasan Warri kafin 2019 – Amaechi

Ministan sufuri Rotimi Amaechi yace an yi nisa a aikin dogon Warri

Rotimi Amaechi ya bayyana mana cewa Gwamnatin Shugaba Buhari tayi nisa a aikin hanyar jirgin kasan da zai ratsa Jihar Kogi har zuwa Jihar Delta da ke Kudu maso Kudancin kasar nan. Layin zai bi ta Itakpe zuwa Ajaokuta har Warri.

Yanzu dai an yi kashi 70 zuwa 80 na aikin kamar yadda Ministan ya fada, Rotimi Amaechi yace ba shakka kafin shekarar 2019 za a gama wannan aikin saboda kwazon da ‘Yan kwangilan su ka sa babu dare babu rana a halin yanzu.

KU KARANTA: Shugaba Buhari yayi alkawarin gyara tituna a Kudancin Najeriya

Bayan nan Rotimi Amaechi ya bayyana cewa Gwamnatin Najeriya ta sa kudi har fiye da Dala Miliyan 200 wajen wannan aiki. Rashin tsaro a Yankin Kudu maso Kudu ne ma dai yake jawo bacin lokacin da ake samu a aikin.

Haka-zalika Gwamnatin Buhari za ta kashe Dala Biliyan 1.5 wajen aikin hanyar jirgin kasan da zai dauko hanya tun daga Legas har zuwa Ibadan. A ka’ida dai shekaru 3 ya kamata a dauka ana aikin amma za a kammala kafin nan.

Dazu kun ji cewa Femi Adesina wanda ke ba Shugaban kasa Buhari shawara kan harkokin yada labarai ya bayyana cewa maganar titi da dogo na jirgin kasa da wutan lantarki ne a gaban Shuugaba Buhari kafin ya bar karagar mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel