Mataimakin Gwamnan Jihar Kano ya fadawa DSS cewa yana cikin babban hadari

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano ya fadawa DSS cewa yana cikin babban hadari

Mun samu labari dazu cewa Farfesa Hafiz Abubakar wanda shi ne Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Dr. Umar Abdullai Ganduje ya kai kuka gaban ‘Yan Sanda cewa ana neman ganin bayan sa a Kano.

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano ya fadawa DSS cewa yana cikin babban hadari

Farfesa Hafiz Abubakar yace yana cikin babban hadari

Farfesa Hafiz Abubakar ya aika takarda zuwa ga Jami’an SSS masu fararen kaya cewa ana kokarin ganin bayan rayuwar sa. Bayan nan kuma Mataimakin Gwamnan na Kano yace ana neman tsige sa da karfin tsiya daga kujerar sa.

Jaridar Daily Nigerian ta bayyana wannan inda ta fitar da wasikar da Mataimakin Gwamnan ya aikawa Rundunar ‘Yan Sanda. Abubakar dai yana tare ne da tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ne duk da yana Gwamnatin Ganduje.

KU KARANTA: Mutanen Arewa ba su ji dadin ziyarar da Kwankwaso ya kai wa wani rikakken ‘Dan adawar Buhari ba

Mataimakin Gwamnan ya bayyana cewa Gwamnatin Ganduje ba ta bas hi matsuguni a gidan Gwamnati ba don haka a ko yaushe ana iya auka masa a gidan sa da ke cikin Gari. Abubakar ya nemi a kara masa Jami’an tsaro.

Hafiz Abubakar a wasikar ta sa ya nuna cewa Ganduje yana kokarin bada kudi domin ayi zanga-zangar cewa ya sauka daga mukamin sa. Dazu dai kun ji cewa Manyan ‘Yan PDP sun yi maraba da dawowar Rabiu Kwankwaso.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel