Yanzu Yanzu: Jakadan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu, Ibeto ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Yanzu Yanzu: Jakadan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu, Ibeto ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Niger kuma jakadan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu, Alhaji Ahmed Ibeto, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar PDP a jihar.

Ibeto wadda ya kasance mataimakin gwamnan tsohon gwamnan jihar Niger Muazu Babangida Aliyu na tsawon shekaru takwas ya sauya sheka ne daga PDP zuwa APC a zaben 2014/2015 bayan ya fadi a zaben fid da gwani.

Yanzu Yanzu: Jakadan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu, Ibeto ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Yanzu Yanzu: Jakadan Najeriya a kasar Afrika ta Kudu, Ibeto ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

A yanzu, Ibeto na kokarin ganin ya samu katin mamba na PDP daga mazabarsa a Ibeto dake karamar hukumar Magma dake jihar.

KU KARANTA KUMA: Benue: Buhari ya nesanta kansa da yunkurin tsige Gwamna Ortom

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Gwamnan jihar Adamawa, Mohammed Bindow, da takwaransa na jihar Niger, Abubakar Bello, sun yi watsi da rade-radin dake yawo cewa suna kokarin sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

Gwamnonin sun bayyana matsayarsu a wani zantawa da suka yi da manema labarai a lokuta daban-daban a jihohinsu.

Bindow yayi Magana a yayinda yake amsa wata tambaya akan lamarin a lokacin day a dawo Yola, babban birnin jihar bayan wani ziyara da ya kai Abuja a ranar Litinin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel