Kotu ta tisa keyar wasu ma'aikatan INEC zuwa gidan kurkuku

Kotu ta tisa keyar wasu ma'aikatan INEC zuwa gidan kurkuku

- Ana zargin su da barnatar da kudi kimanin naira miliyan 179.8

- Hukumar EFCC ta mika su ga wata babbar kotu dake jihar Lagos

Kotu ta tisa keyar wasu ma'aikatan INEC zuwa gidan kurkuku

Kotu ta tisa keyar wasu ma'aikatan INEC zuwa gidan kurkuku

Wasu jami'an hukumar zabe guda uku sun shiga hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa, inda ita kuma ta mikasu ga wata babbar kotu dake jihar Lagos don gabatar da hukunci a gare su a bisa laifin da suka aikata na karkatar da kudi kimanin naira miliyan 179.8.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta mikasu ga wata babbar kotu dake jihar Legas karkashin alkalancin Justice Muslim Hassan.

DUBA WANNAN: Dubun wasu 'yan fashi ta cika, yayinda sojoji suka yi sukuwar sallah a kansu

Jami'an da hukumar yaki da cin hanci da rashawan ta kama sun hada da Yemi Akinwonmi, Dickson Atiba da kuma Ogunmodede Oladayo wadanda suka gurfana a gaban kotu a ranan Litinin dinnan data gabata.

Hukumar EFCC ta samu nasarar cafke wadanda ake zargin da kwasar kudi miliyan N179.8.

hukumar ta EFCC ta kara da cewa wannan laifi ya sabawa doka sannan za'a hukuntasu akan sashe na 15 a dokar kasa.

Alkali Hassan ya dage sauraron karar zuwa 6 ga watan Augustan nan da zai kama.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel