Dubun wasu 'yan fashi ta cika, yayinda sojoji suka yi sukuwar sallah a kansu

Dubun wasu 'yan fashi ta cika, yayinda sojoji suka yi sukuwar sallah a kansu

- An kama su dauke da munanan makamai

- Daya daga cikin su ya rasa ransa a lokacin da suke musayar wuta da Sojojin

Dubun wasu 'yan fashi ta cika, yayinda sojoji suka yi sukuwar sallah a kansu

Dubun wasu 'yan fashi ta cika, yayinda sojoji suka yi sukuwar sallah a kansu

Sojojin Nageriya sun kama wasu yan fashi guda Biyar a garin Felele dake kan hanyar Lokoja zuwa Okene.

A cewar mai magana da yawun rundunar sojin, Brig. Gen. Texas Chukwu yace an kama wadanda ake zargin su badda kamanni ta hanyar sanya kakin soja.

DUBA WANNAN: Ba kada Ganduje ne a gabanmu ni da Kwankwaso ba – Shekarau

Chukwu yace uku daga cikin wadanda aka kama sun hada da Saviour Denis mai shekaru 39, Isaac Donald mai shekaru 35 da kuma Joseph Isah mai shekaru 35 yayinda daya daga cikin su ya rasa ransa a lokacin da suke musayar wuta da Sojojin.

Biyu daga cikin su mata ne Janet Isah da Oyinoye Ochefije.

An kama su dauke da munanan makamai wadanda suka hada da bindiga mai kirar AK 47, da harsashai guda 28 da kuma kakin soja guda Hudu.

Sannan an samesu da adduna guda biyu, kakin 'yan sandan, takalmi guda daya da kuma wayoyin sadarwar guda 22.

Chukwu ya kara da cewa an samesu da kudi kimanin naira 16,980.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel