Benue: Buhari ya nesanta kansa da yunkurin tsige Gwamna Ortom

Benue: Buhari ya nesanta kansa da yunkurin tsige Gwamna Ortom

Fadar shugaban kasa ta nesanta Shugaba Muhammad Buhari daga yunkurin da wasu 'yan majalisar dokokin APC marasa rinjaye na jihar Benue ke yi na son tsige Gwamnan Jihar, Smuel Ortom.

Shugaban kasar ya jaddada cewa ba zai goyi bayan duk wani mataki da ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa ba.

Buhari ya yi nuni da cewa a can baya, an yi zamanin da marasa rinjaye a majalisa kan tsige gwamna, matakin da ya saba tsarin dokar kasa inda yace gwamnatinsa ba za ta lamunci karya tsarin mulki ba.

Benue: Buhari ya nesanta kansa da yunkurin tsige Gwamna Ortom

Benue: Buhari ya nesanta kansa da yunkurin tsige Gwamna Ortom

Ya kuma kara da cewa wasu makiyansa ne ke kokarin alakanta shi da rikicin jihar Benue.

KU KARANTA KUMA: Bamu da niyan barin jam’iyyar APC – Gwamnonin Adamawa da Niger

A halin da ake ciki, Legit.ng ta ruwaito a baya cewa Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi, yace jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kebbi a shirye suke don yakar kowa da katunan zabensu don tabbatar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo kan karagar mulki a 2019.

Yace mutanen jihar sun yarda da sake zabar Buhari a zaben shugabancin kasa mai zuwa saboda jajircewarsa wajen ganin ya dawo da martabar kasar a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel