Za mu sayar da dukkanin kadarorin da muka ƙwato hannun 'Yan harambe - Buhari

Za mu sayar da dukkanin kadarorin da muka ƙwato hannun 'Yan harambe - Buhari

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta kudiri aniyyar sayar da kadarorin da ta ƙwato daga hannun 'yan harambe da kuma barayin gwamnati.

Cikin ofishin jakadancin Najeriya, shugaban kasar yayin amsa tambayoyin 'yan Najeriya dake kasar Togo a daren ranar Lahadin da ta gabata ya bayyana cewa, za a sayar da kadarorin ne kuma a sanya kudaden cikin asusun kasar nan.

Legit.ng ta fahimci cewa, shugaba Buhari tare da tawagar sa sun shilla Birnin Lome na kasar Togo domin halartar muhimman tarukan da suka shafi kungiyar kasashen Afirka ta Yamma.

Za mu sayar da dukkanin kadarorin da muka kwato hannun 'Yan harambe - Buhari

Za mu sayar da dukkanin kadarorin da muka kwato hannun 'Yan harambe - Buhari

Hadimi na musamman ga shugaban kasar akan hulda da manema labarai, Mallam Garba Shehu ya bayyana cewa, gwamnatin shugaba Buhari ta yi tsayuwar daka tare da sake zage dantsen ta wajen cika akawurranta uku da ta dauka yayin yakin neman zabe.

Alkawurran uku sun hadar da samar da ingataccen tsaro, habaka tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari zai ziyarci 'Kasar Togo tare da Ministar Kudi, Kemi Adeosun

Shugaban kasar ya ci gaba da cewa, da a ce gwamnatocin da suka gabata sun ribaci alfanun kaso 25 cikin 100 na kudaden shiga da ake samu a sanadiyar man fetur, to da kuwa 'yan Najeriya ba su yi korafe-korafen da su ke yi a halin yanzu.

Ya kuma sake hikaito yadda wata gwamnatin baya ta salwantar da Dalar Amurka Biliyan 16 wajen samar da wutar lantarki wanda kawowa yanzu lamarin ya kasance tamkar Shuka ta ci Shirwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel