Adamu na hari na ne don ya kare kansa daga EFCC – Saraki

Adamu na hari na ne don ya kare kansa daga EFCC – Saraki

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki a ranar Litinin ya caccaki Sanata Abdullahi Adamu inda ya bayyana shi a matsayin mayaudari kuma makaryaci wadda zai iya yin komai da fadin komai don yak are halin da yake ciki a kowani lokaci.

Saraki na maida martani ne ga wani jawabi da Adamu ya alakanta da shi akan sanata Dino Melaye.

A wata sanarwa da ya saki ta hannun mai bashi shawara na musamman akan harkokin labarai, Yusuph Olaniyonu, Saraki yayi zargin cewa Adamu ya dade yana masa sharri da karairayi amma ya dauke ido saboda ganin girman furfura.

Adamu na hari na ne don ya kare kansa daga EFCC – Saraki

Adamu na hari na ne don ya kare kansa daga EFCC – Saraki

Saraki yace babu yadda za’ayi yayi mugun kalami akan Dino alhalin ya san cewa sanatan ya fi Adamu kokari da yin abun azo a gani a majalisa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Tsoffin shugabannin kasa Obasanjo da Jonathan sun yi ganawar sirri

Saraki ya bayyana cewa maganar Adamu baa bun karba bane balle a yarda da shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel